Jummaʼa 3 Yuli 2026 - 19:49
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (50) | Mahdawiyya A Cikin Alƙur'ani (Kashi Na Biyu)

Hauza / Kasancewa cikin rauni ko zalunci kadai ba shi ne dalilin samun nasara a kan makiya da mulkar kasa ba; a'a, kasancewar imani da samun cancanta su ma sharadi ne na dole. Saboda haka, raunanan duniya ba za su taba samun ikon mulkar duniya ba har sai sun raya wadannan manyan ka'idoji guda biyu.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da wannan jerin tattaunawa kan batun Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ilimi mai alaka da Imamin Zamani (Allah Ya gaggauta bayyanarsa) ga dukkan masu karatu.

Ga wasu daga cikin ayoyin da ke da alaka da Hazrat Mahdi (A.S) da juyin juya halinsa na duniya:

Aya Ta Farko:

«وَلَقَدْ كَتَبْنَا فِي الزَّبُورِ مِنْ بَعْدِ الذِّكْرِ أَنَّ الْأَرْضَ يَرِثُهَا عِبَادِيَ الصَّالِحُونَ»

"Kuma lallai Mun rubuta a cikin Zabura bayan ambato (Attaura) cewa: Lallai zamu gadar da kasa ga bayina na kwarai (Salihai)." (Suratul Anbiya, Aya ta 105)

Wannan aya tana ishara ne ga daya daga cikin mafi bayyanar sakamakon lada na duniya ga mutanen kwarai (mulkin kasa baki daya). A cikin hadisai da dama, an bayyana cewa wannan babban lamari zai faru ne a lokacin bayyanar Imam Mahdi (A.S).

Bayanin Kalmomin Ayar

 «Zabura»: Littafin Annabi Dawuda (A.S) ne (wanda a cikin littattafan Tsohon Alkawari ake kira da "Mazamir Dawuda"). Shi ne: "Tarun addu'o'i, munajat, da wa'azozin Annabi Dawuda (A.S)."

 «Zikiri»: A asali yana nufin abin da ke zama tunatarwa; amma a cikin wannan aya – ta hanyar ambatonsa kafin Zabura – an fassara shi da Littafin Suhuf din Annabi Musa (A.S), wato (Attaura).

 «Ard»: Yana nufin daukacin doron kasa; sai dai idan akwai wata alama ta daban da ke nuna akasin haka.

 «Irsi» (Gado): Yana nufin abin da ke komawa ga mutum ba tare da wani ciniki ko musayar kudi ba. A cikin Alkur'ani mai girma, wani lokacin yana nufin mamaye duniya da samun nasarar al'umma ta kwarai a kan al'umma mabarnata, da mallakar albarkatunsu. (Duba: Suratul A'araf, Aya ta 137).

Ganin yadda aka danganta kalmar "Bayi" zuwa ga "Allah", hakan yana nuna alamun imaninsu da tauhidinsu a fili. Sannan idan aka dubi kalmar "Salihun" (na kwarai), dukkan siffofi na cancanta suna zuwa cikin tunani: Aiki nagari da tsoron Allah, ilimi da basira, iko da karfi, tsari da gudanarwa, da kuma fahimtar zamantakewa.

A lokacin da bayi muminai suka samar da wadannan siffofi na cancanta a tare da su, Allah Shi ma zai taimake su domin su yi nasara a kan masu girman kai.

Saboda haka, kasancewa cikin rauni (Mustad'afin) kadai ba shi ne dalilin samun nasara a kan makiya da mulkar kasa ba; a'a, kasancewar imani da samun cancanta su ma sharadi ne, kuma mustad'afan (raunanan duniya) muddin ba su raya wadannan abubuwa guda biyu ba, ba za su kai ga mulkin kasa ba.

Abubuwan Lura

1. Aali Muhammad (S.A.W.A)

A cikin tafsirin wannan aya mai girma, an samo daga Imam Baƙir (A.S) yana cewa:

«هُمْ آلُ مُحَمَّدٍ یَبْعَثُ اللَّهُ مَهْدِیهُمْ بَعْدَ جَهْدِهِمْ فَیعِزُّهُمْ وَ یذِلُّ عَدُوَّهُمْ»

"Wadannan bayi na kwarai, su ne Aali Muhammad (S.A.W.W). Allah zai aiko da Mahdinsu bayan tsananin kokarinsu, sai Ya daukaka su kuma Ya kaskantar da makiyansu." (Kitabul Ghaibah, Sheikh Tusi, Shafi na 184).

A fili yake cewa ma'anar wannan hadisi ba wai ta takaita ba ce kawai ga su kadai; a'a, yana bayyana mafi kololuwar misali ne na ayar. Don haka, a kowane lokaci da kowane guri idan bayin Allah na kwarai suka mike, za su yi nasara, kuma a karshe su ne za su gaji mulkin kasa.

2. Bisharar Mulkin Mutanen Kwarai a Cikin Zaburar Annabi Dawuda (A.S)

A cikin littafin Zaburar Annabi Dawuda, an samo wannan bayani ko makamancinsa a wurare da dama, wanda hakan ke nuna cewa duk da canje-canjen da aka yi wa wadannan littattafai, wannan bangare ya tsira daga hannun masu canzawa:

 "Miyagu za su yanke, amma masu dogaro ga Ubangiji, su ne za su gaji kasa..." (Zabura, 37, Aya ta 9).

 "Amma masu tawali'u za su gaji kasa, kuma za su yi farin ciki saboda yawan salama." (Zabura, 37, Aya ta 11).

 "Wadanda Ubangiji Ya albarkace su za su gaji kasa; amma wadanda Ya la'ance su za su yanke." (Zabura, 37, Aya ta 22).

 "Masu gaskiya (Siddikai) za su gaji kasa, kuma za su zauna a cikinta har abada." (Zabura, 37, Aya ta 29).

A cikin wadannan kalamai, kalmar "Salihun" (na kwarai) da ta zo a cikin Alkur'ani tana nan da yanayinta a cikin Zaburar Annabi Dawuda. Bayan haka, an ambaci wasu siffofi kamar siddikai, masu dogaro, masu albarka, da masu tawali'u. Wadannan siffofi shaida ne a kan gama-garin mulkin "Salihai" kuma sun dace da hadisan bayyanar Hazrat Imam Mahdi (A.S).

3. Mulkin Mutanen Kwarai: Daya Daga Cikin Dokokin Halitta

Dole ne a sani cewa dukkan mulke-mulke na azzalumai sun sabawa dabi'ar halitta da dokokin sararin samaniya; abin da ya dace da dokar halitta shi ne kawai mulkin mutanen kwarai muminai. Tsarin halitta shaida ce a fili a kan amincewa da ingantaccen tsarin zamantakewa a nan gaba, kuma wannan shi ne abin da ake nufi daga ayar da aka ambata da kuma hadisan da ke da alaka da bayyanar babban mai gyara na duniya. (Tafsiri Namune, Juzu'i na 13, Shafi na 515 - 524).

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ɗauko daga littafin "Darsnameh Mahdaviyyat" na Khodamurad Salimiyan tare da ɗan gyara kadan

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha